Zuri'a 5 mafiya arziki a duniya (Hotuna)

Duk da kasancewar annobar Coronavirus da ta janyo tsayawar al'amura da tilasta kamfanoni rufewa, akwai wadanda arzikin su yaci gaba da karuwa.

Akwai zuri'a masu arziki a duniya da suka sami karin arziki na ban mamaki.

Duba da wannan, Legit.ng ta kawo jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a duniya kamar yadda ta samo daga Bloomberg.

1. Zuri'ar Walton

Zuri'ar Walmart ita ce zuri'a mafi arziki a duniya kiyasin da ya kai dala biliyan 215 kwatankwacin (₦81,958,000,000,000.02)

Zuri'ar suke da Walmart, kamfanin sari mafi yawan kudin shiga a duniya, da siyayayyar da ta kai kimanin dala biliyan 524 (₦199,748,800,000,000.03) daga dakunan shaguna 11,000 a fadin duniya.

Sam Walton ya siye shago na farko a shekarar 1945, kuma bayan rasuwar sa a 1992, babban dan sa da aka sani da Rob ya zama shugaba. Yanzu iyalan sa suna da sama da dala biliyan 215.

2. Zuri'ar Mars

Frank Mars ya kirkiri Mars Incorporated, wani kamfanin Amurka mai hada abincin dabbobi da sauran kayan abinci da kuma maganin dabbobi.

Zuri'ar Mars na da kimanin dala biliyan 120 kwatankwacin (₦45,744,000,000,000.01).

Zuri'ar Mars na da arzikin da ya haura dala biliyan 120.

3. Zuri'ar Koch

Fred Koch wanda dashi aka samar da Wood River Oil and Refining Co a shekarar 1945 kuma yayan sa hudu, Frederick, Charles, David da William suka gaji kamfanin bayan mutuwar sa.

Yan uwan sun samu sabani wajen gudanar da kamfanin a shekarar 1980, tilastawa Frederick da William barin kasuwancin yayin da Charles da David suka tsaya.

Tun daga wannan lokacin kamfanin ya ci gaba da habbaka zuwa Koch Industries, da harajin da ya kai dala biliyan 115 kimanin (₦43,838,000,000,000.01).

Zuri'ar Koch na da kimanin dala biliyan 109.7 kwatankwacin (₦41,817,640,000,000.01).

KU KARANTA: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

4. Gidan Saud

Gidan Saud ne gidan sarautar da ke jagorantar sarautar Saudi Arabia.

Zuri'ar suna da kimanin dala biliyan 95 kwatankwacin (₦36,214,000,000,000.01).

Kiyasin na zuwa ne daga kudin da ake biya sama da shekara 50, daga ofishin sarki.

Iyalan suna da sama da dala biliyan 95.

5. Zuri'ar Ambani

Dhirubhai Ambani shine ya samar da Reliance Industries. Dan sa ne ya ci gaba da kula da dukiyar bayan rasuwar sa a 2002.

Zuri'ar na da kimanin dala biliyan 81.3 kwatankwacin (₦30,991,560,000,000.00).

Masana'antar da ke Mumbai suke da babbar matatar man fetur a duniya. Zuri'ar Ambani suna da sama da dala biliyan 81.3

DUBA WANNAN: Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya

A wani rahoton daban, kun ji tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi'u Kwankwaso ya musanta zargin nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano don cin zarafin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ya yi wannan jawabi ne yana mai mayar da martani ga zargin da Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje ya yi masa, The Nation ta ruwaito.

Ganduje ya yi wannan zargin ne a wurin bikin kaddamar da wata littafi. Ya kuma kara da cewar ko lokacin da a ka nada Sanusi a 2014, ba shi ne mafi cancanta ba. Ya kuma ce an tsige Sanusi ne don kare martabar masarautar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9knJsam5hYse2vsiaZG5lnZazqsXAZpirspmgtm6tjJ2sp6Gplnqpu9OupZpmmKm6rQ%3D%3D