M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - A karshen watan da ya gabata, sababbin gwamnonin jihohin da aka zaba a farkon 2023 suka cika shekara guda a ofis.
Daga zamansa gwamna bayan ya gaji Abdullahi Umar Ganduje, Abba Yusuf ya kawo wasu ayyukan cigaba da-dama a jihar Kano.
Duk da nasarorin gwamnatin NNPP, ana fama da wasu kalubale kamar matsalar ruwa wanda ake sa ran a magance matsalar.
Matakai 10 da Gwamna Abba ya dauka wajen ayyana dokar ta baci a kan ilmi a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu daga cikin ayyukan da za su a yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf sun hada da biyan fansho da giratuti bayan shekaru.
Bayan tsofaffin ma’aikata, gwamnatin Abba ta taba zaurawa da ‘yan matan da aka aurar da su a karkashin tsarin auren gata.
1.Tura dalibai zuwa makarantun kasashen waje
2.Biyan giratuti da fanshon tsofaffin ma’aikata
3.Aurar da zaurawa da ‘yan mata
4.Biyan kudin makarantar wasu daliban Kano da ke jami’o’in gida
5.Rage kudin karatu a manyan makarantun gwamnatin jiha
6.Biyan kudin jarrabawar kammala shiga sakandare
7.Bude makarantun koyon sana’o’in da aka yi watsi da su
8.Karbo da gyaran manyan asibitocin gwamnatin Kano
9.Fara aikin gadojin sama a Dan Aguni da Tal’udu
10.Kwangilolin tituna a cikin unguwanni
11.Farfado da tsarin gina titunan kilomita 5 a kananan hukumomi
Kano: Kwankwaso ya fadi abin da ya dauke hankalin Abba a shekara 1 na mulki
12.Tallafawa mata da masu kananan kasuwanci
13.Haskaka titunan garin Kano
14.Yunkurin daina zaftare albashi da sauran hakkokin ma’aikata
15.Taimakawa marasa lafiya da maganguna da kula kyauta
Da Legit Hausa ta zanta da Hassani Sani Tukur, ya shaida mata cewa a tsarin gwamnatin Kwankwasiyya, ilmi ne a kan gaba.
Hassan Tukur yana cikin masu taimakwa gwamnan jihar Kano a shafin sadarwa ya ce inganta ilmi shi ne burin Abba Kabir Yusuf.
A cewarsa, ilmi yana da muhimmanci kuma sun fahimci da haka ne za a yi maganin mafi yawan matsalolin da suka addabi kasar nan.
A yammacin jiya ne aka ji labari Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa dokar ta-baci, zai gyara makarantu kuma zai gina aji 10, 000 a Kano.
An fara da kara kason ilmi a kasafin kudin 2024, za a bude makarantun da aka rufe kuma gwamnatin Kano ta dauki malaman BESDA.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboN2fI9mpK6gmaK6orqMmrCyrZuWu26wwGaesJmdo661tc1mmJuakWLBosXIZpqio5mjerS0xKSYq5ldZnqiecmin5qqXaCur7uO